Labaran Duniya

Abin Al’ajabi Budurwa ta Koka Kan yadda Maza ke gudun yin soyayya da ita a dalilin fitowar gashi a jikinta

Budurwa ta Koka Kan yadda Maza ke gudun yin soyayya da ita a dalilin fitowar gashi a jikinta 

Wata mata yar Tanzania mai suna Elsie wacce tai fama da wata cuta da ake kira Hirsutism dake jawo fitowar gashi a sassan jiki ta Koka Kan yadda maza ke gudun ta.
Elsie tun tana yarinya take fama da cutar Hirsutism wanda hakan yasa ta fuskanci wahalhalu da kalubale a dalilin cutar.
A wata tattaunawa da aka yi da ita a Kafar sadarwar ta Wasafi, ta bayyana dalilan da yasa maza key gudun ta, basa iya yin soyayya da ita da yadda mutane ke ganin ta a matsayin wacce ta sauya halittar ta.
Mutane da yawa na yi mata kallon wani jinsi daban, musamman wadanda basu san yanayin cutar da ta same ta ba. Hakan yasa maza basa iya nuna mata soyayya.
Wasu lokuta ana tambayar kawayen ta, ita din mace ce ta gaskiya ko kuwa sauya halittar ta tayi, kuma basa iya yin soyayya da ita idan suka Kalli gashin dake jikinta.
Na yarda da kaddarar halittar da Allah yai min, domin ya kaddara hakan ya faru dani don wani dalilin. Kuma nima kamar sauran mata nake, cewar Elsie
Na karbi hakan a matsayin kaddara, amma ina fuskantar kalubale sosai. Mutane da dama na iya ganina a matsayin wata kalar halitta daban, amma ni mace ce kamar sauran dukkan mata

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button